A Malesiya yau kwanan na biyu da ake gudanarda zanga-zanga kin jinin firaministan kasar Najib Razak bisa zarginsa da hannu a wata babbar badakallar karkata akalan wasu kudaden kasar.
Dubun dubatar al’ummar kasar ne suka sake komawa zanga-zanga a yau bayan shafe daren jiyya suna zamen durshin.
Kawo yanzu dai babu wani cikas a zanga-zangar dake gudana duk kuwa da cewa ‘yan sanda kasar sun haramta ta.
Kiraye-kirayen kin jinin Najib Razak dai sun biyo bayan da mujallar Wall Street Journal ta bankado a watan Yuli daya gabata labarin cewa masu bincike a kasar Malasiya sun gano cewa an zubawa firaministan kudade a asusun sa da yawan su kai milliyan 640 na EurO.288